Isa ga babban shafi
Belgium-France

Maharin birnin Paris ya ki magana a gaban kotu

Salah Abdelsalam, daya daga cikin maharan birnin Paris na shekarar 2015, da suka hallaka mutane 130, ya ki amsa tambayoyin da alkalan kotun da ke masa shari’a a kasar Belgium suka yi masa. A yau Litinin AbdeSalam ya sake gurfana a gaban kotun bisa tuhumar yunkurin hallaka jami’an tsaro.

masu gabatar da kara a Faransa na zargin Abdesalam da bayar da gagarumar gudunmawa, a hare-haren Paris, da ‘yan bindiga da ‘yan kunar bakin wake suka kai kan gidajen abinci, filin wasan kwallo da kuma mashaya, inda suka hallaka mutane 130.
masu gabatar da kara a Faransa na zargin Abdesalam da bayar da gagarumar gudunmawa, a hare-haren Paris, da ‘yan bindiga da ‘yan kunar bakin wake suka kai kan gidajen abinci, filin wasan kwallo da kuma mashaya, inda suka hallaka mutane 130. REUTERS
Talla

Salah AbdeSalam wanda ya ki cewa uffan kan tambayoyin da Alkalin kotun ta Belgium ke masa, ya jadda cewa shirun nasa ba wai yana nufin shi mai laifi ba ne, ya yi hakan ne don tsare kan sa, domin ba’a yi wa Musulmai adalci a duk lokacin da ire-iren kotunan ke yi musu shari’a, sai dai Musulman su fuskanci kaskanci da kuma rashin tausayi.

AbdeSalam wanda tun a watan Maris na shekarar 2016, ya ki amsa tambayoyin kotu a kashin farko na shari’ar tasa da aka fara saurara, ya bukaci masu bincike su gabatar da cikakkun shaidun zargin da ake masa, ba wai biyan bukatun son rai ba.

Masu gabatar da kara a Faransa na zargin Abdesalam da bayar da gagarumar gudunmawa, a hare-haren Paris, da ‘yan bindiga da ‘yan kunar bakin wake suka kai kan gidajen abinci, filin wasan kwallo da kuma mashaya, inda suka hallaka mutane 130.

Sai dai shari’ar da kotun Brussels bata shafi hare-haren na Paris ba, ana shari’ar ce kan musayar wutar da yayi da jami’an tsaron Belgium a lokacin da sukai kokarin kamashi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.