rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Italiya Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Dubban 'yan Italiya sun yi zanga-zangar kyama ga akidar wariya

media
Wasu daga cikin dubban ‘yan kasar Italiya yayin da suke zanga-zangar nuna kyama ga akidar nuna wariyar launi a garin Macerata. 10 ga watan Fabarairu, 2018. REUTERS/Yara Nardi

Dubban ‘yan kasar Italiya sun gudanar da zanga-zangar nuna kyama ga akidar nuna wariyar launi a garin Macerata, inda a makon da ya gabata wani dan bindiga ya bude wuta kan bakin-haure ‘yan nahiyar Afrika.


A bayan bayan nan dai tattaunawa kan harin da aka kai wa bakin-hauren ya mamaye yakin neman zaben ‘yan takara a kasar, wadanda zasu fafata a zaben 'yan majalisa da za’a yi a ranar 4 ga watan Maris mai zuwa.

Masu sharhi kan al'amuran siyasar Italiya na kallon batun kwararar bakin-haure cikin kasar a matsayin daya daga cikin manyan al'amuran da zasu yi tasiri a sakamakon zaben.

Sama da bakin-haure daga Arewacin Afrikca dubu 600,000 ne suka ketara takeun Mediterranean zuwa cikin Italiya a cikin shekaru 4 da suka gabata.