rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Mutane 71 sun mutu a hatsarin jirgin Rasha

media
Dusar kankara ta lullube jirgin da ya hatsari a yankin Ramensky na Rasha a ranar Lahadi REUTERS/Stringer

Mutane 71 sun rasa rayukansu bayan jirgin saman da ke dauke da su ya yi hatsari a wajen birnin Moscow na Rasha.Shugaban kasar, Vladmir Putin ya jajanta wa iyalan wadanda hatsarin ya ritsa da su.


Jirgin fasinjan samfurin Antonov An-148 ya gamu da hatsarin ne bayan ya taso daga filin jiragen sama na Domodedovo da ke birnin Moscow da zimmar isa birnin Orsk amma ya yi hatsari a yankin Ramensky.

Masu bincike sun bayyana hatsarin a matsayin daya daga cikin munanan hatsurran jiragen sama da aka gani a tarihin Rasha.

Fasinjoji 65 da kuma jami’ai shida ne ke cikin jirgin, kuma dukkaninsu sun riga mu gidan gaskiya kamar yadda hukumomin Rasha suka tabbatar.

Dusar kankara ta lulllube yankin da hatsarin ya auku, lamarin da ya haifar da jibin goshi ga jami’an agajin gaggawa kafin su isa yankin.

A ‘yan makwannin nan dai, Rasha na fama da matsannaciyar zubar kankara, yayin da masu bincike ke cewa, ba za su yi gaggawar alakanta hatsarin da rashin kyawun yanayi ba.

Tuni aka gano na’urar nadar bayanai na jirgin wato Black Box da za ta taimaka wajen gano musabbabin aukuwar hatsarin.

Shekaru bakwai kenan da kera jirgin wanda kamfanin Saratov Airlines ya siya daga hannun wani takwaransa shekara guda da ta gabata.