rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa ISIL Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ta kafa cibiyoyin killace mayakan Jihadi

media
Shirin dai shi ne irinsa na uku da Faransar ta kaddamar don kawo karshen yaduwar ayyukan ta'addanci a kasar musamman ta yadda kungiyoyin ke yaudarar kananan yara. PHILIPPE HUGUEN / AFP

Gwamnatin Faransa za ta samar da wasu cibiyoyin ajjiye mayakan jihadin da suka dawo don kaucewa watsuwarsu a gidajen yari karkashin wani shirin hana yada tsauraran akidu tsakanin al’ummar kasar.


Shirin wanda aka kaddamar yau Juma’a shi ne irinsa na 3 cikin shekara hudu da Faransar ta aiwatar da nufin jan hankalin jama’a dangane da hadarin tsauraran akidun addini tun bayan hare-haren ta’addancin da suka hallaka fiye da mutane 240 a kasar.

Shirin na da nufin rage yawaitar matasan da ke kwarara cikin cikin kungiyoyin addinin masu da’awar addinin Islama da kasar ke zargin bakin haure da assasawa, ta yadda su ke daukan matasa masu karancin shekaru zuwa kungiyoyi irinsu IS da Alqa'eda.

Firaministan Faransa Edouard Philippe yayin jawaban da ya gabatar gabanin kaddamar da shirin a arewacin birnin Lille ya ce cibiyoyin guda uku za su rika karbar mayakan da suka dawo daga gabas ta tsakiya bayan karya lagonsu a kasashen da suke yaki yayinda za a rika basu kulawa don kaucewa yaduwar akidunsu a cikin al’umma.

Kawo yanzu dai akwai kimanin mutane 512 da ke zaman wakafi kan zargin ayyukan ta’addanci a Faransar yayinda ake kyautata zaton dawowar akalla dubu daya da 139.

A cewar Firaminista Edouard Philippe daga cikin wadanda ake tsare da su yanzu haka har da yaran da shekarunsu basu gaza 13 da haihuwa ba, wadanda ya ce dole ne a basu kulawa ta musamman don ceto rayuwarsu dama ta sauran al’umma.