rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Poland Faransa Birtaniya Canjin Yanayi

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Tsananin sanyi ya kashe mutane a kasashen Turai

media
Dusar kankara za ta haddasa katsewar wutar lantarki da layukan sadarwa kamar yadda hukumomi suka yi gargadi

Akalla mutane 20 sun rasa rayukansu cikin kwanaki hudu sakamakon tsananin sanyi da ake fama da shi a kasashen Turai, lamarin da ya jefa matafiya cikin kunci bayan soke zirga-zirgar ababawan hawa da suka hada da jiragen sama.


Tsananin sanyin na bayan bayan da aka yi wa lakabi da “The beast from East” ya taso ne daga yankin Serbia na Rasha, in da ya mamaye sassan kasashen Turai kamar yadda masu bincike na suka sanar.

Masu hasashen yanayi sun ce, ma’aunin sanyin ya zarce na yankin Arctic, lamarin da ya bai wa kwararru a fannin kimiya mamaki.

A yankin Kudancin Kasashen Turai kadai, an samu asarar rayukan mutane akalla 10, yayin da a jiya kadai ibtila’in ya lakume rayukan mutane biyar a Poland.

Yanzu haka alkaluman mutanen da suka mutu a Poland tun daga watan Nuwamban bara sakamakon tsananin sanyin sun kai 53.

Mahukuntan Birtaniya sun gargadi samun curin kankara mai tsawon sentimita 10 a yau Talata, ganin yadda dusar kankar ke ci gaba da zuba.

Matsalar za kuma ta haddasa katsewar wutar lantarki da layukan sadarwa.

Akalla jiragen sama 60 ne aka soke zirga-zirgarsu a filin jirgi na Heathrow da ke Birtaniya kadai saboda wannan ibtila’in.

Kazalika matsalar ta tsananta a Italiya da Faransa, in da a nan ma ta kashe mutane tare da haddasa curin dusar kankara mai tsawon centimita 15.