rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Amurka Donald Trump Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya fara sharar fagen sake neman shugabanci

media
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Mike Theiler

Shugaban Amurka Donald Trump ya nada Brad Parscale a matsayin Manajan yakin neman zaben sa wa’adi na biyu da za’ayi a shekarar 2020.


Ofishin yakin neman zaben Trump, ya ce Parscale mai shekaru 42, zai mayar da hankali wajen shirya matakan da za’a bi wajen gudanar da yakin neman sake zaben shugaban da kuma fatan samun nasara.

Yayin da yake amsa tambayoyi a gaban zauren majalisar Amurka, Parscale, wanda ya taba zama daya daga cikin jami’an yakin neman zaben Trump a shekarar 2016, ya musanta cewa an samu hadin baki tsakaninsu da wakilan kasar Rasha, domin tasiri a zaben da ya gudana.

Wannan mataki dai na zuwa ne kasa da shekara guda da rabi da Trump ya yi, da fara shugabancin Amurka.

Amurkawa da dama basu yi mamakin bayyana aniyar shugaban nasu na neman a sake zabensa ba.