Isa ga babban shafi
Faransa

Za'a sauya sunan jam'iyyar adawa ta National Front a karshen mako

A karshen makonnan ake sa ran babbar jam’iyyar adawa a Faransa National Front zata sauya sunanta, biyo bayan amincewar daukar matakin da magoya bayan jam’iyyar suka yi, kamar yadda jagorarsu Marine Le Pen ta sanar a ranar Alhamis.

Marine Le Pen jam'iyyar adawa ta National Front, kuma tsohuwar 'yar takarar shugabancin Faransa a zaben 2017.
Marine Le Pen jam'iyyar adawa ta National Front, kuma tsohuwar 'yar takarar shugabancin Faransa a zaben 2017. REUTERS/Pascal Rossignol
Talla

Shugabar Jam’iyyar ta masu zazzafan ra’ayin Marine Le Pen, ta ce magoya bayan jam’iyyar da aka mikawa bukatar dubu 27,000 ne daga cikin dubu 51, 000 suka amince da bukatar sauya sunan jam’iyyar.

Sai dai fa a wata sabuwa, mahaifin jagorar ‘yan adawar Jean-Marie Le Pen, kuma tsohon shugaban jam’iyyar ta National Front, ya zargi ‘yarsa da yin karya dangane da gaskiyar sakamakon alkalumman ‘yan jam’iyyar da suka amince da matakin sauya sunan.

Jean-Marie Le Pen ya bayyana zargin cewa an sauya sakamakon kuri’ar jin ra’ayin yayin da ake kirga kuri’un a sirrance.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.