rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Diflomasiya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Trump ya kori sakataren harkokin wajensa

media
Tsohon sakataren harkokin wajen Amurka da Trump ya maye gurbinsa da Mike Pompeo. REUTERS/Jonathan Ernst/Pool

Shugaban Amurka Donald Trump ya kori sakataren harkokin wajen kasar Rex Tillerson daga mukaminsa.


Sallamar Tillerson ta zo ne Kwana daya bayan da ya kai ziyara zuwa kasashen Najeriya, Chadi, da kuma Kenya.

Trump wanda ya wallafa sanarwar ta shafinsa na Twitter, ya ce daraktan hukumar leken asirin kasar CIA, Mike Pompeo, shi ne zai maye gurbin Tillerson.

Donald Trump ya kuma bayyana Gina Haspel, a matsayin sabuwar shugabar hukumar leken asirin kasar ta CIA.

Har yanzu Rex Tillerson bai ce komai dangane da sallamarsa daga bakin aiki ba, sai dai wani na kusa dashi ya ce tsohon sakataren harkokin wajen Amurkan yana matukar sha'awar aikin da yake yi.