Isa ga babban shafi

Birtaniya zata kauracewa Gasar cin kofin duniya a Rasha

Fira Ministan Birtaniya, Theresa May, ta ce babu wani mai rike da mukamin gwamnatin kasar da suka hada da Ministoci ko ‘yan gidan sarauta da zai halarci gasar cin kofin duniya da za’a yi a Rasha.

Fira Ministan Birtaniya Theresa May.
Fira Ministan Birtaniya Theresa May. Parliament TV handout via REUTERS
Talla

Firaminista May, ta sanar da matakin kauracewa halartar kallon wasan ne yayin da take tsokaci, akan hari da makami mai guba da aka kai wa wani tsohon dan leken asirin Rasha Sergie Skrippal da ‘yarsa Yulia a Salisbury da ke Birtaniya a makon da ya gabata.

Fira Minista May ta bayyana cewa an hada makamin da akai amfani da shi ne a Rasha, kuma akwai yakinin cewa Rashan tana da hannu wajen kai wa Skrippal harin wanda a har yanzu yake kwance a asibiti da ‘yarsa a cikin mummunan yanayi.

Amurka ma ta zargi Rasha da kai harin da makami mai guba da ake kira 'nerve agent' a turance akan wani tsohon jami’in leken asirin kasar da ke Birtaniya, inda ta bukaci kwamitin Sulhu ya dauki mataki akan kasar.

Jakadiyar Amurka a Majalisar, Nikki Haley tace babu shakkah Rasha ce ta kai harin, yayin da Jakadan Rasha a Majalisar Vassily Nabenzia yayi watsi da zargin, ya kuma ya nesanta kasar sa da harin.

Kafin wannan lokacin dai Birtaniya ta sanar da korar jakadun Rasha 23 daga kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.