Isa ga babban shafi
Faransa

Macron na son tabbatar da sauyi ga EU nan da watan Yuni

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kiran samun wani shirin sauyi na musamman ga kungiyar Tarayyar Turai EU nan da watan Yuni mai zuwa. Macron na wannan kira ne yayin ziyarar da Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ke kai wa birnin Paris a yau Juma'a.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwararsa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel bayan kammala taron da suka gudanar yau a birnin Paris wanda ya mayar da hankali kan sauye-sauye ga kungiyar EU.
Shugaban Faransa Emmanuel Macron tare da takwararsa shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel bayan kammala taron da suka gudanar yau a birnin Paris wanda ya mayar da hankali kan sauye-sauye ga kungiyar EU. REUTERS/Francois Lenoir
Talla

Yayin da ya ke jawabi bayan ganawa da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a birnin Paris, shugaba Macron ya bukacin goyan bayan Merkel wajen ganin an samu nasarar sauyin da ya ke bukatar gani a tsarin tafiyar da kungiyar ta EU.

Shugaba Emmanuel Macron dai na ganin ala tilas a aiwatar da sauye-sauyen da suka dace, ganin irin kalubalen da ke gaban kungiyar, musamman ta hanyar samar da Ministan kudi da harkokin kasafin kudi guda daya ga kasashen.

Shugabannin biyu za kuma su tunkari batun rikicinsu da Rasha na baya-bayan nan bayanda Britaniya ta gano hannunta dumu-dumu a kisan tsohon dan leken asirinta da ke aiki da birtaniya a yanzu tare da 'yarsa ta hanyar amfani da wata nau'in guda.

Ziyarar Uwargida Merkel zuwa birnin na Paris a yau Jumaa na nuna yadda kasashen biyu ke da fatan ganin al'amuransu na tafiya kafada-da-kafada musamman kan al'amuran da suka shafi kungiyar EU.

Tuni dai shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana goyan bayan ta ga wa’adin lokacin da Macron ya bukata domin ganin an samu cigaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.