rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Rasha Vladimir Putin

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Al'ummar Rasha suna kada kuri'a a zaben shugaban kasa

media
Shugaban Rasha Vladimir Putin yayin da yake kada kuri'arsa a birnin Moscow, a zaben shugabancin kasar da yake neman wa'adi na 4. Maris, 18, 2018. Sergei Chirkov/POOL via Reuters

Al’ummar Rasha sun fara kada kuri’a a zaben shugabancin kasar, wanda a cikinsa shugaba Vladmir Putin yake neman wa’adi na hudu.


Sakamakon wata kuri’ar Jin ra’ayi da aka gudanar gabannin zaben ya nuna cewa kusan kashi 70 na ‘yan kasar ta Rasha na goyon bayan Putin.

Putin wanda ya ke kan shugabancin Rasha tun daga shekarar 2000, yana fuskantar abokan hamayya bakwai, daga cikinsu akwai attajirin kasar mai ra’ayin gurguzu Pavel Grudinin, Ksenia Sobchak wata tsohuwar ma’aikaciyar talabijin, sai kuma Vladmir Zhirinovsky wani sanannen mai ra’ayin kishin kasa.

Madugun ‘yan adawar kasar ta Rasha Alexei Navalny bai samu shiga zaben ba, sakamakon haramcin hakan da kotu ta yi masa bisa samunsa da laifin aikata almundahana, matakin da Navalny ya bayyana a matsayin makircin siyasa.

Navalny ya kuma bukaci magoya bayansa da su kauracewa zaben shugabancin kasar.