Isa ga babban shafi
Birtaniya

EU ta bukaci Birtaniya ta tsawaita tattaunawar da suke yi

Kungiyar tarayyar turai EU, ta shawarci Birtaniya, da ta kara tsawaita wa’adin da ta debarwa kanta na kammala ficewa daga karkashin kungiyar, domin cimma gamsassun yarjejeniyoyi kan yadda alaka zata kasance tsakaninta da kungiyar musamman akan kasuwanci, bayan ta fice daga cikinta.

Tutar Birtaniya da ta kungiyar tarayyar turai EU a birnin Brussels, Belgium. Disamba 8, 2017.
Tutar Birtaniya da ta kungiyar tarayyar turai EU a birnin Brussels, Belgium. Disamba 8, 2017. REUTERS/Yves Herman
Talla

Tun a watan Maris na 2017, Fira Ministan Birtaniya Theresa May, ta kaddamar da shiri na karshe don fitar da kasar daga karkashin EU cikin shekaru biyu, wato zuwa 29 ga watan Maris na 2019 kenan.

Birtaniya ta kuma bukaci cimma yarjejeniya da EU kan yadda alakar kasuwanci zata kasance tsakaninsu zuwa tana Oktoba, bayan ficewarta daga kungiyar.

Sai dai kwamitin EU mai lura da tattaunawar ya ce abin da kamar wuya a cimma burin da ake bukata acikin takaitaccen lokaci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.