Isa ga babban shafi
Finland

Jami'an tsaro na ci gaba da binciken Puidgemont a Finland

Dan majalisar dokokin Finland Nikko Karna da ya shirya wata ganawa ta musamman da tsohon shugaban yankin Catalonia Carles Puidgemont ya sanarwa jami’an tsaro cewa Puidgemont ya bar kasar tun a jiya Juma’a.

Mr Nikko ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Puidgemonta yayi tafiyar bazata inda ya koma Belgium tare da barin sakon cewa a shirye ya ke ya bayar da hadin kai ga jami’an tsaro a can belgium.
Mr Nikko ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Puidgemonta yayi tafiyar bazata inda ya koma Belgium tare da barin sakon cewa a shirye ya ke ya bayar da hadin kai ga jami’an tsaro a can belgium. REUTERS/Yves Herman
Talla

Jami’an tsaro hadaka sun bukaci kame Puidgemon yayin ganawar ta sa da Mr Nikko ta tsawon kwanaki biyu don tattaunawa da ‘yan majalisun kasar karkashin umarnin kamen da kungiyar tarayyar Turai ta bayar ga ilahirin kasashen Nahiyar.

Sai dai Mr Nikko ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa Puidgemonta yayi tafiyar bazata inda ya koma Belgium tare da barin sakon cewa a shirye ya ke ya bayar da hadin kai ga jami’an tsaro a can belgium.

Jami’an tsaron Finland sun ce sun yi iyakar kokarinsu wajen ganin sun bi umarnin takaddar kamen amma basu gano inda Puidgemon ya boye ba.

Haka zalika hukumar bincike ta NBI ta ce bata gasgata kalaman na Mr Nikko ba, inda ta ce za ta ci gaba da gudanar da bincike la’akari da cewa babu wata shaida da ta nuna cewa Puidgemont ya bar kasar ta Finland a jiya Juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.