rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Nicolas Sarkozy Rashawa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Hukumomin Faransa na bukatar gurfanar da Sarkozy gaban kotu

media
Tsohon shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da ke fuskantar zarge-zargen badakalar cin hanci da rashawa. REUTERS/Ian Langsdon

Hukumomi Kasar Faransa sun bukaci gurfanar da tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy a gaban kotu saboda tuhumar da ake masa na cin hanci da rashawa da kuma kokarin hana alkali gudanar da ayyukan sa.


Mai gabatar da kara ya kuma bukaci lauyan tsohon shugaban Thierry Herzog da wani tsohon mai shari’a Gilbert Azibert da suma su gurfana a gaban kotu akan shari’ar saboda hannun da suke da shi.

Wannan mataki dai ba karamar koma baya bane ga Sarkozy wanda yayi kokarin sake dawowa mulki a watan Nuwambar shekarar 2016 amma bai samu nasara ba.