rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Spain Jamus Catalonia

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Puigdemont ya kalubalanci shirin yi ma sa shari'a a Jamus

media
Carles Puigdemont REUTERS/Yves Herman

Shugaban 'yan awaren Catalonia da ke tsare a Jamus, Carles Puigdemont ya kalubalanci shirin yi ma sa shari’a kan zargin cin amanar kasa, in da yake cewa bai dace a tuhume shi ba.


Lauyan Puigdemont, Jaume Alonso Cuevillas ya bukaci Kotu ta yi watsi da tuhumar da ake ma sa na bore da kashe kudin hukuma ta hanyar da ba ta kamata ba, tare da wata tsohuwar Ministarsa Clara Ponsati.

Tun a makon jiya ne hukumomin kasar Jamus suka kama Puigdemont wanda ke kokarin tserewa ta kasa, sannan kuma suka tsare shi.

Puigdemont dai na fuskantar barazanar tasa keyersa zuwa Spain don yi ma sa shari'a kan laifukan da ake zargin sa da aikatawa da suka hada da cin amanar kasa.