Isa ga babban shafi
Faransa

An gurfanar da wasu matasa biyar da suka je yakin jihadi a Syriya a gaban kotun birnin Paris

Wata kotu a Faransa ta fara sauraren shara’ar matasa 5 da suka je yakin jihadi a kasar Syriya, inda 3 daga cikinsu yan sanda suka gabatar da su a kotun, sauran 2 kuma, suka bayyana dan radin kansu.

A garin Lunel na Faransa  kimanin matasa  20 suka shiga yakin jihadi a Syria
A garin Lunel na Faransa kimanin matasa 20 suka shiga yakin jihadi a Syria REUTERS/Philippe Laurenson
Talla

Garin Lunel ,dake kudancin Faransa, gari ne dake kunshe da mayakan jihadi sama da 20 matasan da yanzu haka suka tafi kasar Syriya da sunan yakin jihadi..

Shara’ar mutanen 5 an fara ta ne a yau alhamis a wata kotu dake birnin paris, ba tare da halartar sauran da ake tuhuma ba su sama da 20 da ake zaton ko dai sun mutu ko kuma suna can suna ci gaba da jidalin a Syriya

A zaman kotun na yau, a kan mambarin uku daga cikin mayakan jihadin 5 ne a halarce da suka hada da Hamza Mosli, Adil Barki da Ali Abdoumi, a yayinda suaran 2 da aka sakaya sunayensu Jawad S. Saad B. sun halarci zaman kotun ne bisa radin kansu karkashin kulawar kotun.

Shidai ayarin matasab ya yi regerigen zuwa yakin jihadi a kasar Syriya ne a tsakanin 2013 da 2014, wanda ya sa ya zama ayari mafi girma na matasan da suka shiga jihadi a Fransa, inda a wannan dan karamin gari na Lunel mai kunshe da mutane dubu 26 ya zama ja gaba, wajen yaye mayakan jihadi, har ya bazu a sauran garuruwan kasar ta Fransa.

Yara matasa da suka yi batan dabo, daga wannan gari na Lunel, sun tafi ne a Syriya inda suka hadu da mayakan kungiyar Jaysh Mohamed (sojojin Muhamad) , wani gungun mayaka dake dauke da makamai karkashin kungiyar Al-Nosra, da ta yi mabaya’a ga kungiyar Al-Qaïda. Da kuma kungiyar Jihadi ta EI ko Isis.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.