rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ireland Birtaniya Amurka

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yankin Ireland na cika shekaru 20 da samun zaman lafiya

media
Ginin Majalisar dokokin Ireland. REUTERS

Yankin Ireland ta Arewa na bikin cika shekaru 20 da yarjejeniyar zaman lafiya mai dimbin tarihi, wanda ya kawo karshen tashin hankalin da aka fuskanta wanda ya lakume rayukan mutane kusan 3,500.


Ita dai wannan yarjejeniyar da aka yiwa lakabi da ‘Good Friday Accord’ da aka kulla ta shekaru 20 da suka gabata, ta yi nasarar kawo karshen tashin hankalin da wannan Yankin ya fuskanta wanda ya kai ga hallaka mutane sama da 3,500.

Yarjejeniyar ta kunshi raba mukaman gwamnati tsakanin kungiyoyin da ke bore domin cigaba da zama a Birtaniya da kuma mabiya darikar Katolika da ke neman hadewa da Ireland.

Firaministan Birtaniya a wancan lokaci, Tony Blair wanda ya jagoranci kulla yarjejeniyar kawo karshen tashin hankalin, zai halarci bikin da za’ayi yau na cika shekaru 20 tare da Jakadan Amurka na musamman wajen shawo kan rikicin, George Mitchell da tsohon shugaban Amurka Bill Clinton da kuma tsoffin shugabannin Ireland da Ireland ta Arewa, Bertie Ahern da Gerry Adams da David Trimble da kuma Peter Robinson.