Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya ta bukaci zaman Majalisar Dinkin Duniya kan makami mai guba

Birtaniya ta bukaci gudanar da taron kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya don tattauna rahotan jami’an hukumar da ke yaki da yaduwar makami mai guba dangane da harin da aka kai da sinadari mai guba kan jami’in leken asirin kasar ta.

Ranar 18 ga watan nan ne ake saran gudanar da taron na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan batun amfani da makaman masu guba..
Ranar 18 ga watan nan ne ake saran gudanar da taron na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya kan batun amfani da makaman masu guba.. ©HO / PRU / AFP
Talla

Rahotan binciken da hukumar yaki da makami mai guba ta gabatar ya tabbatar da zargin da Birtaniya ke yi na cewar Rasha ce ta kai harin da sinadarin da aka kera a kasar ta.

Hukumar ta ce samfirin gubar da aka gudanar da bincike akai ya tabbatar musu da cewar sinadari ne na Navichok da aka yi amfani da shi, kuma Rasha ce ta sarrafa shi, zargin da Rasha ke cigaba da musantawa.

Tuni dai wannan hari ya raba Rashar da kasashen Yammacin duniya wadanda suka kori Jakadun Rasha daga kasashen su.

Ranar 18 ga watan nan ne ake saran gudanar da taron na kwamitin sulhu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.