Isa ga babban shafi
Faransa

Macron ya ce a daina wanka da kamar jirwayi a Siyasar Turai

Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya yi gargadi a kan barazanar da ake fuskanta daga masu fakewa da sunan dimokuradiyya domin shimfida salon mulki irin na kama-karya a yankin Turai da kuma sassan Duniya.

Shugaba Emmanuel Macron na magana da manema labarai a birnin Paris na Faransa ranar 16 ga Afrilu 2018.
Shugaba Emmanuel Macron na magana da manema labarai a birnin Paris na Faransa ranar 16 ga Afrilu 2018. REUTERS/Charles Platiau/Pool
Talla

Macron ya yi wannan kashedi ne lokacin da yake gabatar da jawabi a gaban Majalisar Turai da ke birnin Strasbourg a wannan talata.

Shugaban ya ce dabi’ar da aka san mu da shi ita ce dimokuradiyya wadda a karkashinta ake mutunta juna, ba nuna bambaci ga tsiraru, da cin zarafin jama’a ba, balantana tauye hakkokinsu.

To sai dai wasu na fakewa da dimokuradiyyar domin cusa abubuwan da suka yi hannun-riga da ita, abin da ba za mu taba amincewa ya faru ba.

Wasu na neman fakewa da batun kishin kasa, ana tauye wa jama’a hakkokinsu. Wannan ita ce matsalar da a yau ke neman yaduwa har zuwa yankin Turai, bai kamata mu amincewa ba, domin hakan na nufin cewa mun yarda a jefa nahiyarmu cikin wadi na tsaka mai wuya ne.

Amsar da ya kamata a bayar ita ce, mu nuna masu cewa har kullum, salon tsarin dimukuradiyya ne zai cigaba da yin galaba akan salon dimokuradiyyar irin ta Angulu da kan zabo.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.