rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashe renon ingila na daukar matakan dake karo da auren jinsi

media
Theresa May Firaministar Birtaniya REUTERS/Francois Lenoir

Firaministar Birtaniya Theresa May ta bayyana damuwar ta kan yadda wasu kasashen da Birtaniya ta rena suka sanya dokokin dake karo da auran jinsi guda, inda ta bayyana su a matsayin ba dai dai ba.


Yayin da take jawabi wajen taron shugabannin kasashe 53, akasarin su renon Ingila, May tace irin wadannan dokoki na matukar illa ga rayuwar jama’a, musaman na auran jinsi guda da kuma kare hakkokin mata da yan mata.

Theresa May a matsayin ta na Firaministar Birtaniya, tana nadamar irin wadannan dokoki da kasashen ke aiwatarwa.