Isa ga babban shafi
Faransa

Yan Majalisun Faransa sun tafka mahawara dangane da kamfanin kasar na SNCF

A jiya talata 17 ga watan Avrilu majalisar dokokin Faransa ta gabatar da karatun farko na daftarin dokar da za ta baiwa gwamnati damar aiwatar da sauye sauye ga kamfanin sufurin jiragen kasan kasar SNCF.Daftarin dokar dai, ya kumshi fayyace tare da buda kofa, ga masu son zuba jari a cikin kamfanin jiragen kasan tare da sake fasalta tsarin tafiyar da ayyukan ma’áikatan na SNCF, ya samu amincewar yan majalisar dokokin da gagarumin rinjaye.

Cibiyar Kamfanin jiragen kasa na Faransa,SNCF
Cibiyar Kamfanin jiragen kasa na Faransa,SNCF 法新社
Talla

Bayan share tsawon sao’i 24 ana tafka mahawara a majalisar dokokin kan daftarin dokar da gwamnati ta gabatar domin sake fasalta kamfanin sufurin jiragen kasa na SNCF, ya samu amincewar yan majalisu 454 a kan guda 80. Yan majalisu 29 ne suka kauracewa zaben.

Bayan amincewa da gagarumin rinjaye daga gungun yan majalisun Jam’íyyun kawancen LREM-MoDem mai mulki, gungun yan adawa na Republicain da UDI-Agir, masu tsaka tsakin Ra’ayi, sun amince da daftarin dokar, a yayin da kawancen jam’íyyun yan bangaren hagu 3, da na masu ra’ayin kwaminisanci da yan ra’ayin rikau sun yi watsi da daftarin dokar.

Bugu da kari yan majalisun dokokin gunguna 3 na masu sassaucin ra’ayi 3 sun yi watsi da daftarin, a yayin da jam’iyyun masu ra’ayin kwaminisanci suka soki daftarin da ke kunshe da korar ma’aikata cikinsa .

Tuni dai kungiyar ma’aikatan kwadagon jiragen kasa, ta bayyana sake daura damarar ganin ta tilastawa gwamnatin Macron cin tuwon fashi a kokarin da take na fasalta kamfanin na SNCF da suka ce ya yi hannun riga ga ci gaban rayuwarsu, a karkashin shirin sayar da kamfanin ga yan kasuwa da gwamnati ke shirin yi .

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.