Isa ga babban shafi
Faransa

Zanga-zangar nuna bacin rai a Faransa

Kimanin mutane dubu 119 da 500 ne suka shiga wata zanga-zanga da aka gudanar a sassa daban daban na Faransa don ci gaba da nuna adawa da matakin shugaba Emmanuel Macron na samar da sauye-sauye a ma’aikatun gwamnati kamar yadda ma’aikatar cikin gidan kasar ta tabbatar.

Yan Sandar CRS a kokarin su na tarwatsa masu zanga-zanga a Faransa
Yan Sandar CRS a kokarin su na tarwatsa masu zanga-zanga a Faransa REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Ko a makon da ya gabata jami’an ‘yan Sandan kwantar da tarzoma a kasar sun yi arangama da mutanen da ke adawa da gina wata tashar jiragen sama a yammacin birnin Nantes.

Rahotanni sun ce, akalla ‘yan sanda dubu 2 da 500 aka baza domin fatattakar masu zanga-zangar da suka gina tantuna har suka tare a wurin da aka shirya ginin.

A zanga-zangar ta jiya alhamis wayewar  yau juma'a dai kungiyoyin kwadago sun bayyana cewa, kusan mutane dubu 300 ne suka fito don wannan zanga-zanga a Paris da sauran biranen kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.