Isa ga babban shafi
Faransa

An gano mutane 416 da suka tallafawa ISIL a Faransa

Mahukuntan Faransa sun gano mutane 416 da su ka tallafawa mayakan ISIS da makudan kudade. Wannan na zuwa ne bayan wani taro na kwanaki biyu da ya samu halartar Ministocin kasashen duniya 80 da kuma kwararru 500 don tattauna kan matakan katse hanyoyin samun kudaden shiga na ‘yan ta’adda.

Hukumomin a Faransa sun ce mutanen su fiye da 400 na aikin samarwa kungiyar kudade a kasashe daban-daban.
Hukumomin a Faransa sun ce mutanen su fiye da 400 na aikin samarwa kungiyar kudade a kasashe daban-daban. © AP
Talla

Babban mai shigar da karar ‘yan ta’adda a Faransa, Francois Mollins ya ce, jami’an tsaron kasar sun gano mutane 416 da ke bada tallafi ga mayakan ISIS.

Jami’an tsaron sun kuma gano wasu mutane 320 da ke aikin nema wa ISIS kudade a Turkiya da Libya, sannan daga bisa su tura wa mayakan kudadedn da sula tara musu.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani taro na kwanaki biyu da aka gudanar a birnin Paris karkashin hukumar bunkasa tattalin arziki da ci gaban kasa da zimmar yaki da masu samar wa kungiyoyin ‘yan ta’adda kudade.

Ana saran shugaban Faransa, Emmanuel Macron zai gabatar da jawabin rufe taron wani lokaci a yau Alhamis.

Fadar gwamnatin Faransa da ta gabatar da jawabi ga manema labarai gabanin bude taron, ta kiyasta cewa, kungiyar ISIS na da yawan kudaden da suka kai Dala biliyan daya a shekarar 2014 zuwa 2016.

Kungiyar ta samu akasarin wadannan kudade ne ta hanyar kananan haraji da kudin man fetir ko kuma na sata, yayin da kuma take samun karin tallafi daga kasashen ketare kamar yadda fadar ta bayyana.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.