Isa ga babban shafi
Turai

Tarayyar Turai ta haramta amfani da maganin kashe kwari

Kungiyar Kasashen Turai ta dauki matakin hana kusan daukacin magungunan kashe kwari da ake ganin suna sanadiyar mutuwar kudan-zuma, matakin da masu gwagwarmayar kare muhalli suka jinjina masa. Bincike ya nuna cewa, kudan-zuma na taka rawa da kusan kashi 90 wajen kulla aure tsakanin tsirrai a duniya, amma suna mutuwa saboda yadda ake amfani da magungunan kashe kwari akansu.

Magungunan kashe kwari na haddasa mutuwar kudan-zuma da ke taka rawa wajen kulla aure tsakanin tsirrai
Magungunan kashe kwari na haddasa mutuwar kudan-zuma da ke taka rawa wajen kulla aure tsakanin tsirrai REUTERS
Talla

Kudan-zuma na taka muhimmiyar rawa wajen kulla aure tsakanin tsirrai da kashi 90 cikin 100 a duniya, amma sai dai a ‘yan shekarun nan, suna mutuwa sakamakon wasu matsaloli ciki har da amfani da magungunan kashe kwari a gonakai da ke sarari.

A dalilin haka ne, Kasashen Turai suka kada kuri’ar haramta amfani da wasu sinadarai uku na’uin neonicotinoid da ake amfani da wasu wajen kashe kwarin kamar yadda hukumar gudanarwar kungiyar kasasahen Turai ta sanar.

Sai dai wannan haramcin bai hana amfani da sinadaran ba a wuraren da aka killace da rufi don tattalin wasu na’ukan tsirrai.

Daukan matakin na zuwa ne bayan wani rahoton Hukumar Kula da Tsaftar Abinci ta Turai ya bayyana cewa, sinadaran kashe kwarin na barazana ga wanzuwar kudan zuma na gida da daji.

Gabanin kada kuri’ar haramcin a birnin Brussels, masu gwagwarmayar kare muhalli sanye da kaya launin baki da ruwan kwai, sun gudanar da wani gangami a wajen shalkwatan hukumar EU.

Sai dai a bangare guda, manyan kamfanonin samar da magungunan kashe kwari sun ce, wannan matakin zai cutar da manoma a kasashen Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.