rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Zaben Amurka Donald Trump Rasha

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

An wanke Trump daga zargin alaka da jami'an Rasha

media
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS/Yuri Gripas

Kwamitin majalisar wakilan kasar Amurka, da aka dorawa alhakin bincika zargin hadin bakin jami’an Rasha da kwamitin yakin neman zaben shugaba Trump a 2016, ya ce babu wata shaida da ke nuna zargin da ake yi ya tabbata.


Kwamitin, wanda ya bayyana rahoton nasa a jiya Juma’a, ya ce babu shaidar da ke nuna cewa yarjeniyoyin kasuwanci da Donald Trump ya kulla da wasu kamfanonin Rasha, sun zama tsani ga samar da hadin baki tsakanin yakin neman zabensa da jami’an kasar ta Rasha.

Sai dai rahoton kwamitin ya nuna cewa akwai makusantan Trump da suke da alaka da wasu jami’ai a kasar ta Rasha masu dauke da alamar tambaya.

Shugaban Amurka Donald Trump ya dade yana musanta zargin da ake na hadin baki tsakanin kwamitin yakin neman zabensa da wasu jami’an Rasha a shekarar 2016, wajen kayar da abokiyar hamayyarsa Hillary Clinton a zaben shugabancin kasar.

Cikin sakon da ya wallafa a shafinsa na twitter bayan da kwamitin ya fitar da rahoton, Trump ya bayyana cewa hakan ya kawo karshen bita da kullin da ake dade ana yi masa.

Sai dai ‘yan majalisar wakilan Amurkan daga jam’iyyar Democrats guda 9 da ke cikin kwamitin mai manbobi 22, sun yi watsi da sakamakon rahoton da aka wallafa.

‘Yan majalisar na jam’iyyar Democrats sun zargi takwarorinsu na Repulican da kaucewa bin hanyoyin da suka dace wajen gudanar da bincike akan zargin hadin bakin, tsakanin Trump da jami’an Rasha.