Isa ga babban shafi

'Yan sandan Europol sun lalata kafofin yada manufofin IS

Hukumar ‘yan sandan kasa da kasa ta tarayyar turai Europol ta sanar da samun nasarar lalata wasu kafofin yada farfaganda da kungiyar IS ke amfani da su wajen yada manufofinta a shafin Intanet.

ISIS fighters (AFP / File)
ISIS fighters (AFP / File) AFP
Talla

Jami’an da suka kware a fannin fasahar yanar gizo na rundunar ta Europol da ke Canada da Amurka ne suka samu wannan nasara, inda suka toshe kafafen na IS ciki harda kamfanin dillancin labarai na Amaq da kungiyar ta fi amfani da shi.

Jami’an ‘yan sandan na Europol da suka aiwatar da samamen sun fito ne daga kasashen Belguim Faransa, Romania, Holland da kum Birtaniya.

Shugaban hukumar ‘yan sandan ta tarayyar turai, Rob Wainwright ya ce samamen da aka kaiwa kafafen na kungiyar IS, ya haifar mata da gagarumin koma baya wajen samun saukin jan hankulan matasa ta hanyar amfani da farfaganda.

Kafafen Halumu da Nashir, na daga cikin kafofin dillancin labaran kungiyar ta IS da hukumar Europol ta kai wa samamen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.