rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Sakatariyar harkokin cikin gidan Birtaniya ta sauka daga mukaminta

media
Amber Rudd Tsohuwar sakatariyar dake kula da harkokin cikin gidan Birtaniya REUTERS/Simon Dawson

Sakatariyar dake kula da harkokin cikin gidan Birtaniya Amber Rudd ta sauka daga mukamin ta saboda abinda ta kira yaudarar yan Majalisu kan adadin bakin da aka shirya kora daga kasar, matakin da ake ganin sa a matsayin babban koma baya ga gwamnatin Firaminista Theresa May.


Rudd wadda ta fuskanci matsin lamba kan shirin korar bakin da suka fito daga kasashe renon Ingila, ta shaidawa yan Majalisun cewar babu wani adadi da aka yanke na korar bakin, amma daga bisani ta sanar da saukar ta daga mukamin lokacin da wata wasika ta fito fili wadda ke nuna akasin haka.

A wasikar da ta rubutawa Firaminista, Rudd tace ya dace ace ta fahimci abinda wasikar ta kunsa, saboda haka ta dauki alhakin kuskuren da tayi, kuma ta sauka daga mukamin ta.

Wannan murabus zai girgiza Theresa May wadda ranar juma’ar da ta gabata, ta bayyana cikaken goyan bayan ta ga Sakatariyar.