rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Wasanni Kwallon Kafa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kocin Roma ya sha alwashin lallasa Liverpool

media
Ko a shekaru 34 da suka gabata ma wato gasar cin kofin zakarun Turai ta 1984 Liverpool din ce ta yi waje da Romar. Reuters/Carl Recine

Kocin kungiyar kwallon kafa ta Roma Eusebio Di Francesco ya ce bai fidda ran za su yi nasara akan abokiyar karawarsu Liverpool ba har ma su kai ga zagayen karshe na gasar cin kofin zakarun Turai a wasan da za su fafata a gobe Laraba, bayan tun farko Liverpool din ta lallasa su har gida da ci 5-2.


Matukar dai Roma na bukatar kai wa ga wasan karshe na cin kofin zakarun turan a ranar 26 ga watan Mayu to fa lallai sai ta zurawa Liverpool akalla kwallaye har uku ba ko daya a wasan na gobe Laraba, wanda kuma ake ganin abu ne mai matukar wahala la’akari da yadda Muhammad Salah ke ruwan kwallaye.

Ko da ya ke dai a cewar Di Francesco ko wasan da suka kara da Barcelona wanda ya kai su ga nasarar fitar da ita daga gasar ya bai wa mutane mamaki, ganin yadda da farko suka faro kamar za su sha kaye amma daga bisani suka yi waje da Barcelonar, inda a cewarsa kamar hakan ne za su yiwa Liverpool.

Ko a shekaru 34 da suka gabata ma wato gasar cin kofin zakarun Turai ta 1984 Liverpool din ce ta yi waje da Romar.