rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Amurka Tarayyar Turai Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Muna gaf da laftawa kamfanonin Amurka haraji - EU

media
Shugabar hukumar kasuwanci ta Tarayyar Turai Cecilia Malmstrom. REUTERS/Yves Herman

Kungiyar Turai, ta ce tana cikin shirin mayar da martani matukar shugaba Donald Trump ya bayar da umurnin fara aiki da sabon tsarin biyan haraji a kan karafan da yankin ke shigarwa Amurka, wanda ya kamata ya fara aiki daga wannan Talata.


Shugabar hukumar kasuwanci ta Tarayyar Turai Cecilia Malmstrom, ta ce sun shirya tsaf domin mayar da martanin da ya dace daga wannan Talata.

Da farko dai shugaban na Amurka, ya yi wa kasashen na gungun Turai sassauci domin biyan harajin kashi 10 a maimakon 25%, to sai dai wannan sassauci ne na gajeren lokaci da zai kawo karshe a wannan Talata.

Tuni dai Kungiyar ta Turai ta tsara jerin sunayen kamfanonin Amurka da ita ma za ta lafta wa sabon haraji, da suka hada da kamfanonin sarrafa karafa domin kere-kere, masu sarrafa tufafi, na barasa da sauransu.

Shugaba Donald Trump, ya ce an tsananta haraji a kan karafan da ake shiga da su cikin Amurka daga Turai da sauran kasashen duniya ne, domin bai wa kamfanonin Amurka kariya daga mamaya.