rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Shugaban Air France yayi murabus

media
Jean-Marc Janaillac Shugaban kamfanin Air France mai murabus AFP/Eric Piermont

A Faransa bayan kasa kawo karshen yajin aiki da ya mamaye bangaren sufurin jiragen saman kasar Shugaban Kamfanin jiragen sama na Air France Jean Marc Janaillac ya sanar da sauka daga mukamin shugabancin wannan kamfani.


Rashin samun amincewar shugabanin kungiyoyin kwadagon kamfanin Air France musaman ta bangaren kara musu albashi da wasu batututuwa makamancin haka tun bayan da suka tsuduma a cinkin yajin aiki kusan watanni biyu da suka gabata nay a janyo murabus na Shugaban.

Jean Marc Janaillac mai shekaru 65 da aka nada a matsayin Shugaban kamfanin Air France a ranar 6 ga watan yuli na sheakara ta 2016 zai gabatar da takardar saukar sa zuwa kwamity gudanarwa tareda kiran taron da zai kai ga nada sabon Shugaban kamfanin ranar 9 ga wannan watan da muke cikin sa.