rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Bakin-haure Hakkin Dan Adam

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Kasashen turai na tafka muhawara akan rarraba bakin-haure

media
Wasu daruruwan bakin-haure da ke kokarin ketarawa cikin kasar Hungary daga Serbia, yayinda 'yan sandan kasar ta Hungary suka kafa shingen hanasu shiga. Reuters/Marko Djurica

Kasashen Turai sun fara tafka mahawara kan shirin rarraba bakin haure a tsakaninsu, kafin taron shugabannin kasashensu da za’ayi a watan Yuni domin cimma matsayin bai daya a karon farko a cikin shekaru kusan 3.


Rikicin raba bakin-haure da kowacce kasa zata karba ya raba kan kasashen dake kungiyar Turai, musamman a tsakanin wadanda ke kudancin nahiyar dake karbar bakin da suka tsallake teku da kuma wadanda ke makotaka da Yankin kasashen Balkan dake kin karbar bakin.

Kasashe masu arziki irin su Jamus na bukatar ganin kowacce kasa a nahiyar turan ta taka rawa wajen karbar bakin kamar yadda kungiyar kasashen ta EU ta kayyade.

Sabuwar yarjejeniyar da ake so a aiwatar na bukatar ganin kowacce kasa taki karbar bakin da suka nemi mafakar siyasa, sai dai dauko bakin da aka tantance daga wuraren da aka shirya domin kaisu Turai, da kuma baiwa kowacce kasa euro 30,000 domin kula da mutum guda.

Kasashen Poland da Hungary sun ki amincewa da shirin na Turai, abinda ya sa za’a gudanar da taro a makon gobe don cimma yarjejeniyar da za’a mikawa shugabannin nahiyar a taron su na watan gobe.