rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Wani mahari dauke da wuka ya jikata mutane a Paris

media
Lamarin tsaro a kasar Faransa Reuters

Hukumomin yan Sanda a birnin Paris na kasar Faransa sun bayyana mutuwar mutum biyu bayan da wani mutum ya dabawa mutane da dama wuka kafin jami'an tsaro sun harbe shi har lahira.


Rahotanni sun ce mutane sun razana inda suka yi ta kutsawa shagunan sayar da abinci domin kaucewa harin wanda aka kai shi a yankin Opera dake tsakiyar Paris.

Ya zuwa yanzu dai babu cikakken bayani a kan maharin da kuma dalilinsa na kai harin.