rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Birtaniya Tarayyar Turai

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Yan Majalisun Scotland sun kada kuri'ar kin amincewa da ficewar Birtaniya daga EU

media
Theresa May Firaministar Birtaniya REUTERS/Hannah McKay

Majalisar Scotland ta kada kuri’ar kin amincewa da shirin Birtaniya na ficewa daga cikin kungiyar kasashen Turai, matakin da ake ganin zai jefa rudani a yankin.


A taron baya da ya gudana Brussels Shugabannnin Kungiyar Tarayyar Turai 27 sun amince da sabbin sharuddan yarjejeniyar hulda da Birtaniya bayan ficewarta daga nahiyar.Mai shiga tsakani a tattaunawar ficewar, Michel Barnier ya ce, sun dauki hanyar cimma matsaya game da wannan yarejeniya mai sarkakiya.

A cikin watan Mayun shekarar 2019 ne, Birtaniya za ta raba gari da Kungiyar Kasasehen Turai, amma masu shiga tsakani sun amince kan yarjejeniyar ficewar da ta kunshi ci gaba da tattalin zumuncin da ke tsakanin Birtaniya da sauran kasashen na Turai.

Yan Majalisu 93 suka kada kuri’ar kin amincewa da ficewar, yayin da 30 kacal suka goyi baya.