rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Birtaniya Faransa Jamus Muhalli

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

EU ta maka manyan mambobinta a kotu kan gurbata iska

media
Gurbacewar iska ta yi sanadiyar mutuwar mutane dubu 399 a shekarar 2014 REUTERS/Dado Ruvic

Kungiyar Tarayyar Turai ta shigar da karar wasu kasashe 6 manbobinta a kotu, ciki har da Jamus da Faransa da Birtaniya bisa samun su da laifin kin mutunta dokokin tarayyar Turan na daukar matakan rage gurbatar Iska.


Sauran kasashe ukun da suka fuskanci fushin Kungiyar Tarayyar Turan, sun hada da Italiya da Hungary da kuma Romania.

A watan Janairun da ya gabata ne dai EU ta bai wa kasashen 6 dama ta karshe da su dauki matakan magance gurbata yanayin iska a nahiyar Turan, sai dai a cewar shugaban Hukumar Lura da Muhallin Kungiyar Karmenu Vella, kasashen sun gaza daukar matakan da za su gamsar cewa suna kokarin mutunta dokokin da aka shata.

Wata kididdiga ta Kungiyar Tarayyar Turai ta nuna cewa gwamnatocin nahiyar na kashe Euro biliyan 20 a duk shekara domin magance matsalolin lafiya da ke cikawa  da jama’a a dalilin gurbacewar Iskar shaka.

Kazalika gurbatar Iska ta yi sanadin hallakar rayukan mutane dubu 399 a shekarar 2014 kadai.