rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Tarayyar Turai Iran

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Turai za su kare yarjejeniyar Iran daga lalacewa

media
Le ministre iranien des Affaires étrangères, Mohammad Zarif (2e à gauche) entouré (de gauche à droite) par Federica Mogherini, la chef de la diplomatie européenne, et ses homologues français, allemand et britannique, à Bruxelles, ce 15 mai 2018.. REUTERS/Yves Herman

Shugabannin kasashen Turai sun amince da daukar matakin bai daya domin kare yarjejeniyar nukiliyar Iran bayan ficewar kasar Amurka.


Shugabannin sun sha alwashin bai wa Iran duk taimakon da take bukata muddin ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar da ta kulla a shekarar 2015. Shugabannin na kasashen Turai 28 sun bayyana cewar za su ci gaba da kare kasar Iran daga duk wata barazana muddin ita kuma ta ci gaba da mutunta yarjejeniyar da ta kulla.

Shugabannin sun amince da shirin kare kamfanonin kasashen Turai da tuni suka samu kwangiloli a Iran domin kaucewa takunkumin da Amurka ta sanyawa kasar.

Taron ya kuma amince kan yadda zai magance matsalar cewar Iran na fadada ikon ta a gabas ta tsakiya da gina makamai masu linzami da kuma abinda zai biyo baya lokacin da yarjejeniyar nukiliyar za ta daina aiki a shekarar 2025.

A karshe shugabannin sun amince su mayar da martini kan harajin da Trump ya sanya musu wajen cinikin karafa.