Isa ga babban shafi

Kungiyoyin kwadago sun ci gaba da yajin aiki da zanga-zanga a Faransa

Kasar Faransa na shirin fuskantar karin harkokin sufuri sakamakon matsalar yajin aikin ma’aikata da za’a cigaba da yi a cikin wannan mako.

Wasu kungiyoyin kwadago yayin gudanar da zanga-zanga a Paris.
Wasu kungiyoyin kwadago yayin gudanar da zanga-zanga a Paris. REUTERS/Benoit Tessier
Talla

Kungiyoyin ma’aikata 9 dake dauke da mabiya sama da miliyan 5 da rabi suka kira yajin aikin da kuma zanga zanga domin cigaba da adawa ga shirin sauye sauyen gwamnati da kuma korafi kan albashi da makomar ma’aikata 120,000 da shirin zai raba da ayyukan su.

Yau Talata, ana saran gudanar da zanga zanga har kashi 130 a fadin kasar, yayin da a birnin Paris zata gudana daga Place de la Rèpublique da misalign karfe 2 na rana zuwa Place de la Nation.

Karo na uku kenan da kungiyoyin ma’aikatan ke gudanar da zanga-zanga tun bayan zaben shugaba Emmanuel Macron.

Ana saran shugabannin manyan kungiyoyin kwadagon kasar na CGT da FO da kuma CFDT su shiga jerin gwano tare, karo na farko tun bayan shekaar 2010 da suka kalubalanci dokar fansho tare.

Ana saran yajin aikin zai yi illa ga harkokin sufuri da kuma makarantu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.