Isa ga babban shafi
EU

Faransa za ta fice daga matsalar gibin kasafin kudi

Kungiyar Tarayyar Turai ta tsayar da shawarar janye Faransa daga cikin jerin kasashen da ke fama da matsalar gibin kasafin kudi a Turai. Wannan na zuwa ne bayan Faransa ta shafe sama da shekaru 10 ta na fama da matsalar.

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya taka rawa wajen ganin kasar ta yi hannun riga da matsalar gibi a kasafinta a Turai,
Shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya taka rawa wajen ganin kasar ta yi hannun riga da matsalar gibi a kasafinta a Turai, Ludovic Marin/Pool via Reuters
Talla

Ana ganin shugaban Faransa Emmanuel Macron ne ya tsaya kai da fata don samun amincewa daga Jamus wadda ke hankoron ganin an kakaba wa Faransa dokar tsuke bakin aljihu.

Hukumaar Tarayyar Turai ta bukaci a janye Faransa daga tsarin matsanancin gibin kudaden wanda aka fara kaddamarwa a shekarar 2009, lokacin da kasashen da ke amfani da takardar kudi na Euro suka tsindima cikin tarin basuka.

Kwamishinan Harkokin Tattalin Arzikin Tarayyar Turai, Pierre Moscovici ya shaida wa manema labarai cewa, wannan wani lokaci ne mai matukar muhimmanci ga Faransa bayan tsawon shekaru 9 tana cikin wahalar tsarin gibin kudi a kasafinta.

Hukumar Tarayyar Turai dai ta yi hasashen cewa, Faransa za ta samu gibin kashi 2.6 a ma’aunin tattalin arzikinta na GDP a bara, adadin da ya yi kasa da kashi 3 cif cif da EU ta kayyade.

Kazalika a bana, EU na da hasashen cewa, Faransan za ta kai kashi 2.3, sannan kuma a badi ta kai kashi 2.8.

Faransa da Spain ne kadai ke ci gaba da fuskantar barazanar amfani da matsanancin tsarin gibin kudaden da ka iya kai wa ga kakaba musu takunkumai da kuma cin su tara daga Kungiyar Tarayyar Turai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.