Isa ga babban shafi
Faransa

Ma'aikata 140,000 sun yi zanga-zanga a Faransa

Dubun dubatar ma’aikata ne suka gudanar da yajin aiki da kuma zanga-zanga tsawon jiya Talata a sassan kasar Faransa, inda suke nuna rashin amincewa da sauye-sauyen da shugaban kasar Emmanuel Macron ke kan aiwatarwa a tsarin ayyukan gwamnati.

Dubban ma'aikatan Faransa yayin zanga-zangar adawa da sauye sauyen shugaba Emmanuel Macron ga fannin kwadago.
Dubban ma'aikatan Faransa yayin zanga-zangar adawa da sauye sauyen shugaba Emmanuel Macron ga fannin kwadago. REUTERS/Christian Hartmann
Talla

A wannan karo dai illahirin kungiyoyin kwadagon kasar ne suka bukaci magoya bayansu da su shiga yajin aikin, lura da irin matakan da shugaba Emmanuel Macron ke dauka domin samar da sauyi kan tsarin daukar ma’aikata, biyan su albashi da kuma lokacin da ya kamata su je ritaya.

Akalla ma’aikata dubu 140 ne suka yi tattaki a kan titunan biranen kasar ta Faransa, sai dai a birnin Paris an bayyana cewa adadin ma’aikatan da suka shiga jerin gwanon bai wuce dubu 15 ba.

Ma’aikatan gwamnati kusan milyan 6 ne ke nuna fargaba dangane da sauye-sauyen da gwamnatin Macron ke dauka, inda suke cewa sannu a hankali karkashin wadannan sauye-sauyen ana neman maye gurbin cikakkun ma’aikatan gwamnati da wadanda aka yi aro ko kuma ‘yan kwantaragi.

Ministan kwadagon Faransa Olivier Dussopt, ya ce tabbas gwamnati za ta cigaba da aiwatar da sauye-sauyen, amma kuma za a aiwatar da su ne a cikin tsari na doka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.