rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ireland

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Ana gab da soke Dokar hana zubar da ciki a kasar Ireland

media
A woman looks at a new mural of Savita Halappanavar with flowers placed beneath it put up on the day of the Abortion Referendum on liberalising abortion laws in Dublin, Ireland May 25, 2018. 路透社。

An gudanar da zaben raba-gardama kan Dokar hana zubar da Ciki a kasar Ireland, zaben da ya nuna masu son a sauya Dokar sun yi rinjaye da sama da kasha 66.


Sakamakon farko na zaben raba-gardama da aka gudanar dangane da Dokar tsaurara hana zubar da ciki a kasar Ireland ya nuna sama da kashi 66 suna goyon bayan sauya fasalin Dokar da ta hana a zubar da ciki baki daya.

Sakamakon da aka fitar daga 4 daga cikin mazabu 40 ya nuna yadda kashi 66.36 suka amince a yayin da kashi 33.64 suka nuna kin amincewa a yayin da aka samu yawan fitowar jama’a a zaben da ya kai kashi 62 kamar yadda babbar cibiyar zabe ta tsakkiyar birnin Dublin ta bayyana inda aka samu masu goyon baya da yawansu ya kai kashi 77.