Isa ga babban shafi
Italiya

Giuseppe Conte ya kasa kafa gwamnati a kasar Italiya

Mutumin da aka ba wa damar zama Fira Minista idan ya iya hada kan kusoshin gwamnatin kasar Italiya da shugaban kasar mai fuskantar matsaloli Sergio Mattarella ke jagoranta wato Giuseppe Conte ya sallama damar da aka bashi, bayan da ya kasa cimma burin da aka sanya a gaba.

Newly appointed Italy Prime Minister Giuseppe Conte speaks to the media after a consultation with President Sergio Mattarella at the Quirinal Palace in Rome, Italy, May 23, 2018.
Newly appointed Italy Prime Minister Giuseppe Conte speaks to the media after a consultation with President Sergio Mattarella at the Quirinal Palace in Rome, Italy, May 23, 2018. Reuters/路透社
Talla

Dama dai bisa al'ada shugaban kasar kan kira wani amintacce ne ya bashi damar kafa gwamnati ta hanyar hada kan muhimman mutane a kasar ta Italiya, abinda ya sa wannan lokacin aka bai wa shi Conte damar kafa tashi gwamnatin, amma bayan kokarin da ya yi na harhada kawukan muhimman mutanen ya ci tura, daga bisani ya ce ya bada gari.

Conte mai shekaru 53 Lauya kuma dan siyasa a kasar ta Italiya, ya ce ya yi duk komkarin da ya dace ya yi, amma hakan ya ci tura, don haka ya mika wuya.

To sai dai duk da wannan kasawar ta Conte, na da damar gabatar da sunayen mutanen da aka zaba da aniyar nada su a matsayin ministocinsa idan har ya iya kafa gwamnatin.

A labaran da muka sama daga baya sun tabbatar mana cewar yanzu kuma shugaban kasar ya sake kiran wani mutum na daban tare da bashi damar tafiya ya kafa gwamnatin.

Wanda aka zaba din dais hi ne Carlo Cottarelli, kuma za su gana da shugban kasar a ranar Litinin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.