rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Jamus Bakin-haure

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Masu kyamar baki da Musulunci sun yi zanga-zanga a Jamus

media
Bangarori biyu da ke da banbancin ra'ayi kan baki da Musulunci sun yi zanga-zanga a Jamus REUTERS/Hannibal Hanschke

Dubban masu zanga-zangar goyan bayan 'yan ra’ayin rikau da ke kyamar baki da kuma addinin Islama suka halarci wani gangami a Berlin, yayin da masu adawa da su suma suka gudanar da tasu a gefe guda.


Jami’an tsaro dai sun sanya shingaye a tsakanin bangarorin adawar don kauce wa samun sabanin da zai kai ga rikici, yayin da daga bisani suka yi amfani da hayaki mai sanya hawaye don tarwatsa su bayan da yawansu ya fara wuce kima.

Tun da farko, jam’iyyar AfD mai kyamar Musulmi ce ta kira zanga-zangar wadda ke da nufin matsa kaimi don samar wa Jamus makoma mai kyau.

A cewar wata ‘yar jam’iyyar ta AfD Christine Moessl, galibin ‘yan cirani da ke tsallako musu cikin kasa Musulmai ne da a cewarta, su ne ummul aba’isin lalacewar Jamus, la’akari da cewa ba sa martaba mata.

Bangaren jam’iyyar ta AfD dai na rike ne da kwalaye masu rubutu da ke cewa dole Merkel ta tafi wasu kuma na cewa ba ma maraba da baki, yayin da wasu ke cewa Jamus tasu ce ba ta baki ba.

Sai dai a bangaren masu matsakaicin ra’ayi, suma a akwai kwalayen da suka rike dauke da rubutun da ke cewa, ba sa maraba da nuna wariya, wasu kuma na cewa a kawao karshen ‘yan Nazi.