rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Gasar Cin Kofin Duniya Rasha Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa ba za ta haska gasar cin kofin duniya ga al'umma a Majigi ba

media
Yanzu haka dai dubban masu sha'awar kallon ya zama musu wajibi ko dai su kalla a gida ko kuma su je gidajen cinima da ke sassan kasar. Reuters/路透社

Faransa ta dakatar da shirinta na haska wasannin cin kofin duniya kai tsaye a manyan allunan majigi na gefen tituna da dandali ga al'ummar kasar wanda bisa al’ada ta saba yi. A cewarta matakin na da nufin bayar da kariya daga ayyukan ‘yan ta’adda.


Bisa al’ada dai faransar kan haskan wasannin kai tsaye a dandali ko gefunan titi na biranen kasar da nufin saukaka masu sha’awar kallon yadda ta ke wakana a gasar ta cin kofin duniya.

Ma’aikatar harkokin cikin gida ta ce matakin ya zama dole don kare rayukan dubban ‘yan kasar daga ayyukan ta’addanci.

Acewar ma’aikatar, ‘yan ta’addan ka iya amfani da damar wajen salwantar da rayukan mutanen da basu jib a basu gani ba, la’akari da yadda dubban masoya kwallo kan taru.