Isa ga babban shafi
Spain

Jagoran Jam'iyyar gurguzu ya zama Firaministan Spain

A kasar Spain, an nada jagoran Jam'iyyar gurguzu wato Socialist, Pedro Sanchez a matsayin sabon Firaminista bayan da Majalisar kasar da jefa kuri'ar yankan kauna kan tsohon Firaminista Mariano Rajoy. Bangaren jam'iyyar 'yan gurguzun ta samu nasara ne da akalla kuri'u 180.

Pedro Sanchez shi ne shi ne mutum na farko da ya gabatar da kudirin kawar da wanda ya gada wato tsohon Firaminista Mariano Rajoy saboda zargin cin hanci da rashawa da ya shafi babbar jam'iyyar da ke mulki.
Pedro Sanchez shi ne shi ne mutum na farko da ya gabatar da kudirin kawar da wanda ya gada wato tsohon Firaminista Mariano Rajoy saboda zargin cin hanci da rashawa da ya shafi babbar jam'iyyar da ke mulki. REUTERS
Talla

Sabon Firaminista Pedro Sanchez, wanda yanzu haka ke da shekaru 46 an haife shi ne ranar 29 ga watan Fabrairu na shekarar 1972 a birnin Madrid na kasar Spain, inda kuma ya tsunduma jam'iyyar ma'aikata ta Spain wato Spanish Socialist Workers Party a shekarar 1993.

A shekara ta 1995 ne kuma ya kammala karatun jami'a fannin nazarin tattalin arziki da kasuwanci a wata jami'a mai zaman kanta da ke cikin Jami'ar Complutense da ke Madrid babban birnin kasar.

Mr Sanchez ya rike mukamin akawun majalisar dokokin Spain a shekarar 1998, daga bisani kuma bayan shekara guda aka nada shi jagoran wani ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Bosnia yayin yakin Kosovo.

A tsakanin shekarar 2004 zuwa 2009 ya rike mukamin kansila a birnin Madrid yayinda a ya zama wakilin majalisar kasar tsakanin shekarar 2009 zuwa 2011 aka kuma sake zabensa a 2017.

Pedro Sanchez shi ne shi ne mutum na farko da ya gabatar da kudirin kawar da wanda ya gada wato tsohon Firaminista Mariano Rajoy saboda zargin cin hanci da rashawa da ya shafi babbar jam'iyyar da ke mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.