Isa ga babban shafi
NATO

Dakarun NATO da na Amurka sun yi atisayen hadin guiwa a Poland

Akalla Dakaru dubu 18 daga kasashe 19 mambobin kungiyar tsaro ta NATO ne suka fara wani atisayen hadin-gwiwa karkashin jagorancin Amurka a kasar Poland.

Sojin saman kasar Faransa a atisayen dakarun tsaro na NATO
Sojin saman kasar Faransa a atisayen dakarun tsaro na NATO Reuters/路透社
Talla

A wani mataki na karfafa aikin dakarun hadakar na NATO da Amurka ne aka gudanar da wannan atisayen, to sai dai Rasha wadda ke makotaka da Poland na kallon atisayen a matsayin wata babbar barazana a gare ta.

Atisayen sojin karkashin jagorancin Amurka wanda zai kai ranar 15 ga watan Yuni ana gudanarwa, na zuwa ne a dai dai lokacin da Poland ke shirye-shiryen amincewa da wani kudurin Amurka na girke wata bataliyar sojinta ta din-din-din a kasar ta Poland.

Ko a makon daya gabata ma ministan tsaron Poland ya bayyana cewa, kasar za ta kashe dala biliyan guda da rabi zuwa biliyan 2 don bayar da kariya ga rundunar wadda za ta shafi bangaren makaman na Amurka da sauran muhimman kayakin yaki.

Sai dai tuni matakin ya fuskanci kakkausar suka daga Rasha wadda ta ce matakin ba zai haifar da Da mai ido ga kasashen nahiyar ba, haka zalika Rashar ta bayyna matakin atisayen da wani salo ne da za a yi amfani da shi wajen kai mata hare-haren makamai masu linzami.

Kowacce shekara NATO karkashin Jagorancin Amurka kan jagoranci atisayen sojin a Poland yayinda kasashen Jamus Birtaniya da kuma Canada kan jagoranci makamantan shi a kasashen yankin Baltic da suka kunshi Estonia Latvia da kuma Lithuania.

Rasha dai ta ce girke bataliyar Amurkar a Poland ya sabawa yarjejeniyar soji ta 1987 haka kuma ka iya zama babbar barazana ga nahiyar fiye da barazanar yakin cacar bakan da ta gudana tsakanin nahiyoyin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.