rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Faransa Mali Sahel Ta'addanci

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron ya bukaci cika alkawarin da aka yi na tallafawa G5 Sahel

media
Kawo yanzu dai daga cikin kasashen da suka yi alkwarin tallafawa rundunar Saudi Arabia ce kadai ta cika ta hanyar bayar da yuro miliyan dari. REUTERS/Grigory Dukor

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bukaci kasashen duniya da suka yi alkawarin bada agajin kudi da kayan aiki ga rundunar G5 Sahel da ke yaki da ta’addanci a Mali da su gagaguta cika alkawarin su.


Shugaba Macron ya shaidawa manema labarai bayan ganawa da shugaban Nijar Mahamadou Issofou cewar babu abinda su ke bukata cikin gaggauwa da ya wuce kudaden da rundunar za ta yi aiki da su.

Macron ya ce kudin da kungiyar kasashen Turai ta bayar anyi amfani da su wajen fara aikin rundunar, amma yanzu haka suna bukatar karin kudade.

Shugaban Nijar Mahamadou Issofou ya ce suna bukatar gabatar da euro miliyan 420 da akayi alkawari wajen gidauniyar taimakawa rundunar.

Issofou ya ce ya zuwa yanzu kasar Saudi Arabia ce kawai ta cika alkawarin ta na bada euro miliyan 100 wanda za’ayi amfani da su wajen sayan kayan aiki ga dakarun.