Isa ga babban shafi
Turai

Trump ya bukaci mayar da Rasha cikin kasashen G7

Shugaban Amurka Donald Trump, ya bukaci kasashe 7 masu karfin tattalin arziki wato G7, su maido da Rasha cikinsu, wadda suka kora daga kungiyar shekaru 4 da suka gabata, bisa dalilai na Diflomasiyya.

Shugaban Amurka Donald Trump.
Shugaban Amurka Donald Trump. REUTERS
Talla

Yayin ganawa da manema labarai a Washington a yau Juma’a, a lokacin da yake shirin tashi zuwa Canada, Donald Trump yace za ‘iya yiwuwa wasu su kalli bukatar maido da Rasaha cikinsu a matsayin abin da bai da ce, amma a zancen gaskiya kasashen na G7 suna bukatar Rasha a cikinsu domin tattaunawa akan muhimman batutuwa dadama.

A shekarar 2014 ne dai kasashe 8 masu karfin tattalin arziki G8 suka kori Rasha daga cikinsu, suka koma kungiyar G7, bayan da Rashan ta mamaye yankin Crimea da ke karkashin Ukraine.

Yayinda ake bude taron na G7 a yau Juma’a dai, babban abinda zai fi daukar hankali shi ne, yadda za ta kaya tsakanin Amurkan da sauran takwarorinta, wato Faransa, Canada, Jamus, Birtaniya, Italiya, sai kuma Japan, a dalilin takun sakar da ke tsakaninsu, bayan da Amurkan ta kakaba haraji akan kayayyakin aluminium da karafa da kasashen ke shigar da su cikinta, dalilin da ya sa kasashen suka mai da martani, ta hanyar kakaba nasu harajin kan wasu kayayyakin da Amurkan ke kai wa kasashen.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.