rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Donald Trump Emmanuel Macron G7 Tattalin Arziki

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Macron ya zargi Trump da rashin dattako

media
French President Emmanuel Macron listens during a joint press conference with Israeli Prime Minister Benjamin Netanyahu (not pictured) at the Elysee Palace in Paris, France, June 5, 2018. REUTERS/Philippe Wojazer/Pool

Shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya yi gargadin cewa ba za a taba samun dai daito a fuskar diflomasiyya ba, ta hanyar wani ya rika bayar da umarni cikin gadara da fushi.


Macron na maida martani ne ga kalaman shugaban Amurka Donald Trump da ke bayyana takwaransa na Canada Justin Trudeau a matsayin mara adalci, kuma raggo, inda kuma Trump ya janye goyon bayansa ga ga matsayar da kasashen G7 suka cimma akan saisaita huldar cinikayya tsakaninsu, bayan taron da suka kammala a jiya.

Yayin da yake ganawa da manema labarai bayan taron, Fira ministan Canada Justin Trudeau, ya jaddada adawarsa ga harajin da Amurka ta kakabawa abokan huldar ta na turai kan karafa da aluminum, inda fira ministan ya ce ranar 1 ga watan Yuly, Canada za ta fara aiwatar da na ta martanin.

Bayan sauraron jawabin na fira minista Trudeau ne, shugaba Trump ya sanar da janye sa hannunsa akan maslahar da sauran kasashen na G7 suka cimma, kan wasu batutuwan diflomasiya musamman kan saukaka huldar cinikayya tsakaninsu.