rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Ukraine

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Faransa da Jamus za su magance rikicin Ukrain

media
Angela Merkel avec le président ukrainien Petro Porochenko, le 10 avril 2018 à Berlin. REUTERS/Hannibal Hanschke

A kokarin dunke barakar da ake fama da ita a kasar Ukrain mai fama da ‘yan tawaye masu goyon bayan kasar Rasha, kasashen Faransa da Jamus sun amince su hadu da bangarorin masu hamayya da juna domin lalabo zaren magance matsalar.


Ministocin harkokin wajen kasashen Ukraine da Rasha za su hadu da na kasashen Jamus da Faransa yau a birnin Berlin na kasar Jamus domin kokarin magance rikicin Ukraine wanda ya raba bangarorin biyu.

Ya zuwa yanzu dai akalla mutane 10,000 suka rasa rayukan su a rikicin na Ukraine tsakanin masu goyan bayan Rasha da ke neman ballewa daga kasar da kuma dakarun gwamnatin.

Shugaba Vladimir Putin ranar alhamis ya yi gargadi kan duk wata takala daga Ukraine a daidai lokacin da kasar ke shirin fara daukar nauyin gasar cin kofin duniya da za’a fara a wannan makon.

Fadan da aka yi tafkawa shekaru da dama da suka gabata a tsakanin 'yan tawaye da dakarun gwamnatin kasar Ukrain ne ya kai ga harbo jirgin Jigilar kasar Malaysia da har yanzu ba'a san ko wa za'a dora wa laifi ba.

A kwanan nan dai an ambato wasu kasashen Turai na dora laifin ga kasar Rasha, a yayin da Rashar ke cewar su gabatar da hujja da shaidu mai karfi a maimakon magangannun fatar baki.