rfi

Saurare
  • Labarai Kai-tsaye
  • Labaran da suka gabata
  • RFI duniya

Austriya

wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa

Musulmin Austria sun koka da shirin rushe masu masallatai

media
'Yan sanda a wani babban masallaci a ranar Idi AFP

Kungiyar Musulman kasar Austria ta yi Allah wadai da matakin da gwamnatin kasar ta dauka na rufe wasu Masallatai 7 da kuma shirin korar limamansu daga kasar.


Mai Magana da yawun kungiyar Ibrahim Olgun ya ce matakin gwamnatin wani yunkuri ne na batawa addinin Islama suna.

Jami’in ya ce har ya zuwa yanzu gwamnati bata gabatar musu da wata shaida dake danganta Masallatan ko kuma limaman su da zargin da take musu ba.

Austiriya dai ta yi barazanar rufe manyan masallatai 7 da ke a wasu sassan kasar ne, tare kuma da saka wa manyan Limamai 60 Takunkumin hana su kowace irin da'awa.

Shima shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya bayyana matakin a matsayin kyamar addinin Islama, inda yayi akawarin mayar da martani.

Hukumomi a kasar ta Austiriya dai na zargin kungiyoyin musulmin da masallatan ne da karbar kudaden tallafi daga wata kasar waje wato Turkiyya ta hanyar wata kungiya mai ayyukan yada al’adun kasar Turkiyya, wadda ita kuma reshe ce daga ma’aikatar kula da harkokin addinin musulunci ta kasar ta Turkiyya.