wanda aka wallafa • Wanda aka canza zuwa
Emmanuel Macron ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Italiya

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi kakkausar suka ga gwamnatin Italiya sakamakon kin karbar wasu daruruwan baki da suka isa kusa da gabar ruwan kasar amma suka share tsawon kwanaki suna gararamba saboda mahukuntan kasar sun hana su izinin sauka.
Mai magana da yawun shugaban na Fransa Benjamin Griveaux, ya ce Macron ya bayyana wa taron majalisar ministocinsa a yau Talata cewa, matakin da Italiya ta dauka ya yi hannun riga da yarjeniyoyin kasa da kasa da ke tausaya wa wadanda suka sami kansu a irin wannan yanayi.
Italiya ta mayar da martani da cewa babu wani abin koyi da za ta dau daga Faransa.